Kotun A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Masu Juyin Mulki A Kasar

Wato kotun soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ta yanke hukuncin kisa kan mutane 37 da suka hada da Amurkawa 3 da ‘yan kasashe Turai 3

Wato kotun soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ta yanke hukuncin kisa kan mutane 37 da suka hada da Amurkawa 3 da ‘yan kasashe Turai 3

Wata kotun soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane 37 da suka hada da Amurkawa 3 da wasu ‘yan kasashen Turai 3, a shari’ar yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar tun a watan Mayun da ya gabata.

Alkalin kotun, Manjo Freddy Ehomi, ya bayyana cewa: Kotu ta yanke hukuncin kisa ne bayan tabbatar da samun wadanda ake zargi da laifin gudanar da juyin Mulki a kasar, yayin da yake karanta hukuncin da aka yanke wa mutane 37 daga cikin 51 da ake tuhuma hukuncin kisa.

Daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin har da wasu ‘yan kasashen waje guda shida, uku daga cikinsu Amurkawa ne, baya ga wani dan kasar Belgium, da dan kasar Birtaniya, da kuma dan kasar Canada.

A cikin daren Lahadin ranar 19 ga watan Mayu ne, birnin Kinshasa fadar mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya fuskanci tarzomar wasu mutane da dama dauke da makamai da suka kai hari kan gidan minista Vital Camerhi, wanda ya zama shugaban majalisar dokokin kasar, kuma a yayin arangama da jami’an tsaron kasar an kashe ‘yan sanda biyu da ke gadinsa. Bayan haka, maharan sun kai hari kan “Fadar kasa”, gidan tarihi mai dauke da ofisoshin shugaban kasar, Felix Tshisekedi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments