Yemen: Sojojin Kasar Sun Kakkabo Wani Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake sarrafashi Daga Nesa

Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa na gwamnatin Amurka a safiyar yau Litinin, wanda kuma shi ne irinsa na

Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa na gwamnatin Amurka a safiyar yau Litinin, wanda kuma shi ne irinsa na uku da suka kakkabo a cikin mako guda.

Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar Yemen na cewa jirgin saman yakin samfurin MQ-9 Reaper ne, kuma yana iya kai hare hare da makamai masu linzami da aka dora masa, har’ila yau yana da kayakin aikin leken asiri.

Labarin ya kara da cewa farashin ko wanne daga cikin jaragen ya kai dalar Amurla miliyon 35, sanna sojojin yamen sun kakkabo guda 10 daga cikinsu daga fara yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ya zuwa yanzu.

Labarin ya kara da cewa a wannan karon sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin ne a lardin Dhamar daga yammacin kasar ta Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments