Hamas Ta Zargi Amurka Da Rashin Yin Matsin Lamba Ga Isra’ila Don Kawo Karshen Yakin Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta tabbatar da cewa ta na son gudanar da mulkin hadin gwiwa na Falasdinawa na yankin Gaza da aka yi

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta tabbatar da cewa ta na son gudanar da mulkin hadin gwiwa na Falasdinawa na yankin Gaza da aka yi wa kawanya bayan kawo karshen yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Osama Hamdan mamba a ofishin siyasa na kungiyar ya tabbatar da cewa kungiyar na son gudanar da mulkin hadin gwiwa na Falasdinawa na yankin Gaza.

Mista Hamdan ya shaida wa AFP daga Istanbul cewa: ” dole ne Falasdinawa su jagoranci kan su.

Ya Ce ‘’Mun je birnin Beijing, mun yi shawarwari a matsayinmu na Falasdinawa kuma mun amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa don tafiyar da harkokin Falasdinu a Gaza, wadda Hamas ke mulki tun shekara ta 2007.

Jami’in na Hamas ya kuma zargi Amurka da rashin yin matsin lamba ga Isra’ila don kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, wanda ya shiga wata na goma sha biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments