Al-Houthi: Martani na gaba a kan Isra’ila sai ya fi muni

Shugaban kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya tabbatar da cewa, farmakin da dakarun  kasar Yemen na yau wanda aka kai da

Shugaban kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya tabbatar da cewa, farmakin da dakarun  kasar Yemen na yau wanda aka kai da wani makami mai linzami na zamani, ya yi nasarar ketare dukkanin tsarin tsaron makiya, duk da tazarar kilomita 2,040 da ke tsakanin wurin da aka harba makamin da kuma inda ya sauka a birnin Tel Aviv na Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Yayin da yake jawabi ga jerin gwanon miliyoyin mutane a fadin kasar ta Yemen, dangane da zagayowar lokacin maulidin Manzon Muhammad (SAW), Sayyed al-Houthi ya tabbatar da cewa dakarun Yaman ne suka gudanar da wannan farmaki ta hanyar amfani da wani sabon makami mai linzami na cikin gida, yana mai tabbatar da cewa wani bangare ne na kashi na biyar na farmakin kasar a kan Isra’ila, wanda kuma zai ci gaba matukar dai Isra’ila bata kawo karshen kisan kiyashi a Gaza ba.

Da wannan ne jagoran na kungiyar Ansarullah Sayyed al-Houthi ya kara jaddawa wa Isra’ila da masu mara mata baya cewa, abin da yake tafe yafi wannan nesa ba kusa ba.

A halin da ake ciki, Sayyed al-Houthi ya ba da tabbacin cewa sojojin Yemen za su ci gaba da yakin da suke yi a tekun da jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila, Amurka da Birtaniya, “inda suke gudanar da ayyukan da suka samu nasara da tasiri matuka.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments