Iran Ta Maida Martani Kan Kalamin Jami’in Al-Amuran Harkokin Waje Na Tarayyar Turai (EU)

Gwamnatin kasar Iran ta musanta zargin Tarayyar Turai kan cewa kasar ta dulmuya kanta a cikin yakin da ke faruwa a Ukraine. Tashar talabijin ta

Gwamnatin kasar Iran ta musanta zargin Tarayyar Turai kan cewa kasar ta dulmuya kanta a cikin yakin da ke faruwa a Ukraine.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naser Kan’ani yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa “ duk wani labari dangane da cewa Iran ta sayarwa kasar Rasha makamai karya ce”.

A cikin makon da ya gabata ne Josept Borrel jaimi’i mai kula da al-amuran harkokin waje na kasashen Turai yana fadar haka, amma kan’ani ya kara nanata cewa: Abinda na fada shi  ne matsayin jumhuriyar musulunci ta Iran: Duk wata zance ta cewa Iran ta sayarwa Rasha makamai kariya ce.

Kasashen yamma daga ciki har da kasar Amurka da kuma kasashe 3 na Turai, wato Faransa da Jamus da kuma Ingila wadanda aka fi saninsu da E3 suka zargi kasar Iran da aikawa kasar Rasha makamai masu linzami, ba tare da sun gabatar da wani dalili ba, suka kuma dorawa kasar takunkuman tattalin arziki. Daga ciki sun dakatar da yarjeniyar ziraga zirgan jiragen sama na kasar Iran wato ‘IranAir’ zuwa wadannan kasashe sun kuma dakatar da nasu jiragen zuwa kasar Iran.

Kan’ani ya kara da cewa wadan nan takunkuman ba zasu amfana ba, sai dai suna kara tsananta matsalolin da ke tsakanin kasashen da Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments