Rahotonni sun bayyana cewa: Yariman shugaban kungiyar ta’addanci ta Al-Qa’ida yana raye
Rahotonnin sun jaddada cewa: Hamza bin Laden, dan Osama bin Laden, shugaban kungiyar Al-Qa’ida da aka kashe a kasar Pakistan, ya sake bayyana a kasar Afganistan, inda yake kokarin sake farfado da kungiyar Al-Qa’ida da ta durkushe bayan halaka shugabanninta.
A shekara ta 2019 hukumar leken asiri ta Amurka CIA ta yi ikirarin cewa: An kashe Hamza bin Laden. Yayin a halin yanzu haka wasu sabbin rahotannin leken asirin kasashen yammacin duniya suka bayyana cewa Hamza bin Ladan yana shugabantan wani sansanin horo a kasar Afganistan, inda yake kokarin hada kan kungiyar Al-Qa’ida domin daukar fansar kisan mahaifinsa da wasu kwamandojin Amurka suka yi.
Rahotannin da suke fitowa daga kafafen yada labaran Yamma da suka nakalto daga majiyar leken asirin Amurka na cewa: Hamza bin Laden na shirin hada kan dakarun Afghanistan ‘yan kungiyar ISIS, Al-Qa’ida da kuma Taliban domin sake kunna wutar yaki kan kasashen Yamma.
Binciken masana yana nuni da cewa: Hamza bin Laden, wanda aka fi sani da “Yariman Ta’addanci,” yana nan a raye, kuma a asirce yana jagorantar kungiyar ta’addanci da ke da alhakin kai hare-haren ta’addanci da dama, ciki har da munanan ta’addancin da mahaifinsa ya shirya a ranar 11 ga watan Satumba, a cewar shafin “Daily Mail” na kasar Birtaniya.