Gwamnatin Kasar Rasha Ta Kori Jami’an Diblomasiyyar Kasar Burtania 6 Daga Kasar Saboda Zargin Ayyukan Leken Asiri

A jiya Jumma’a ce kafafen yada labarai da jaridun kasar Rasha suka bada labarin cewa gwamnatin kasar ta kori jami’an diblomasiyyar kasar Burtania 6 daga

A jiya Jumma’a ce kafafen yada labarai da jaridun kasar Rasha suka bada labarin cewa gwamnatin kasar ta kori jami’an diblomasiyyar kasar Burtania 6 daga kasar tare da zarginsu da ayyukan leken asiri.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Mariya Zakharova na cewa, gwamnatin kasar Rasha ta sami shaidu kan cewa wani bangare na ma’aikatar harkokin wajen kasar Burtaniya ya tura wadannan jami’an diblomasiyya 6 ne don su yi mata ayyukan leken asiri.

Zakharova ta kara da cewa gwamnatin kasar Rasha ba zata amince da duk abinda zai cutar da mutanen kasar ba. Amma gwamnatin kasar Burtaniya ta musanta hakan, ta kum kara da cewa dalilin da gwamnatin kasar Rasha ta bayar na korar wadan nan jami’anm diblomasiya ba gaskiya bane. Sannan ta yi barazanar itama zata kori wasu daga cikin jami’an diblomasiyyar kasra Rasha daga kasar.

Tun lokacinda sabon Firai ministan kasar Burtania Keir Starmer ya kai ziyara kasar Amurka inda ya tattauna da shugaba Biden dangane da yaki a Ukraine, musamman dangane da damar da suka bawa Ukraine na amfani da makamansu masu linzami kuma masu cin dogon zango, aka fara tada jijiyoyin wuya tsakanin kasashen da Rasha.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya girgadi kasashen turai da Amurka kan cewa idan sun bawa Kiev damar amfani da makamai masu linzami kan kasar Rasha, to kamar kungiyar tsaro ta NATO ta shelanta yaki a kan Rasha ne, don haka daga lokacin yaki a Ukraine zai sauya salo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments