Iran Ta Bayyana Yadda Dangantakarta Da Hukumar IAEA Take Tafiya A Taron Hukumar A Vienna

Jakadan kasar Iran a hukumomin IAEA da take a cibiya a Vienna ya yi karin bayani kan yadda dangantakar kasar da hukumar take a halin

Jakadan kasar Iran a hukumomin IAEA da take a cibiya a Vienna ya yi karin bayani kan yadda dangantakar kasar da hukumar take a halin yanzun da ake gudanar da taron fasali-fasali na hukumar a birnin Vienna.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohsen Naziri yana fadar haka, ya kuma kara da cewa: A ko yaushe kasar Iran tana bukatar tattaunawa don warware matsalolin da ke tasowa tsakanin ta da hukumar ta IAEA.

Naziri ya kara da cewa a taron gwamnonin kasashen kungiyar a fasalin da ya gabata, kasashenn Jamus, Faransa da kuma Ingila sun gabatar da zargi kan kasar Iran dangane da yarjeniyar NPT da kuma shirin makamashin nukliya na kasar, sannan gwamnonin ba tare da sauraron bangaren JMI ba suka yi allawadai da kasar Iran.

Jakadan ya kara da cewa, a halin yanzu gwamnatin kasar Iran ta bada dama wa hukumar ta kakkafa na’urorin daukar hotuna har guda 6 ga hukumar, daga ciki hard a wanda yake daukar ayyukan tache makamacin uranium.

Sannan ya ce yana fatan a duk lokacinda za’a tattauna dangane da kasar Iran a wannan taron gwamnonin hukumar zasu yi amfani da hankali don daukar mataki a kan kasarsa. Idan ba hakaba Iran tana iya maida martani wanda ba zai yi masu dadin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments