Iran Ta Yi Kakkausar Suka Ga Zarge-zargen EU Game Da Ba Rasha Makaman Linzami

Iran, ta yi kakkausar suka ga zargen-zargen kungiyar tarayyar turai, game da batun ba Rasha makamai masu linzami. A cikin wata sanarwa da ya fitar

Iran, ta yi kakkausar suka ga zargen-zargen kungiyar tarayyar turai, game da batun ba Rasha makamai masu linzami.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Juma’a kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naser Kan’ani ya yi kakkausar suka kan kalaman babban jami’in kungiyar tarayyar turai na zargin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da tsoma baki a rikicin kasar Ukraine.

Kan’ani ya ce duk wani ikirari na sayar da makami mai linzami na Iran ga Rasha ba shi da tushe.

“Ina sake tunatar da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fili. Duk wani ikirari na cewa Iran na sayar da makami mai linzami ga kasar Rasha karya ce,” inji shi.

“Muna ba da shawarar cewa Tarayyar Turai ta guje wa zarge-zargen karya,” in ji kakakin. 

Ya kuma yi tsokaci kan barazanar da kungiyar EU ke yi na daukar sabbin matakai kan Iran kan wannan batu.

Tuni dai kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus suka kakaba wa Iran takunkumin karya tattalin arziki, duk da cewa Iran din ta musanta hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments