Kasar Chile ta shigar da bukata a hukumance ga kotun kasa da kasa ta ICJ cewa ta shiga cikin shari’ar da ake yi wa Isra’ila, kamar yadda kotun da ke birnin Hague ta sanar a ranar Juma’a.
A ranar 29 ga watan Disamba ne kasar Afirka ta Kudu ta shigar da kara kan Isra’ila a gaban kotun ta ICJ, kusan watanni uku bayan da gwamnatin mamayar ta kaddamar da hari a kan Gaza.
Koken ya bukaci alkalan kotun da su bayyana cewa Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza tare da umurtar gwamnatin kasar da ta daina kai hare-hare kan mutane.
Nicaragua, Colombia, Mexico, Libya, Falestine, da Spain duk sun gabatar da bukatar shiga cikin shari’ar kuma suna jiran amincewar ICJ don shiga cikin karar.
Kotun kasa da kasa ta tabbatar da cewa ta karbi bukatar Chile a ranar Alhamis.
Tuni dai Hamas ta yi marhabin da sanarwar da Chile ta bayar ta shiga cikin shari’ar kisan kiyashin da ake yi wa Isra’ila wadda Afirka ta Kudu ta shigar a kotun kasa da kasa (ICJ) kan yakin da take yi da Gaza.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce sanarwar ta Chile ta nuna matsayinta ga bil’adama, da kuma watsi da keta dokokin kasa da kasa.
Kungiyar Falasdinu ta kuma yaba wa shugaban kasar Chile, Gabriel Boric saboda “taimaka wa ‘yancin al’ummar Falasdinu da gwagwarmayar neman ‘yanci da cin gashin kansu.”
Hamas ta bukaci kasashen duniya da su shiga shari’ar kisan kare dangi da ake yi wa Isra’ila a gaban kotun ICJ da kuma kara matsa lamba kan Isra’ila kan ta dakatar da yakin da take yi a Gaza.