Yemen Ta Sanar Da Tarwatsa Jiragen Ruwa 80 Na Yahudawa Da Masu Alaka Da Su Daga Nuwamba

Dakarun Yemen sun kai hare-hare kan jiragen ruwa 80 da suke na gwamnatin mamaya da masu alakada ita tun watan Nuwamba Dakarun kasar Yemen da

Dakarun Yemen sun kai hare-hare kan jiragen ruwa 80 da suke na gwamnatin mamaya da masu alakada ita tun watan Nuwamba

Dakarun kasar Yemen da ke gudanar da ayyukansu a teku sun yi barna ga jiragen ruwa da suke da alakada haramtacciyar kasar Isra’ila sama da 80, ta hanyar nutsar da wasu jiragen ruwa guda biyu, sannan kuma sun kwace wasu daga watan Nuwamban shekarar 2023 da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa: Tun a watan Nuwamban shekara ta 2023, sojojin kasar Yemen suka kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki kan jiragen ruwan dakon kaya da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya a tekun Bahar Maliya, Tekun Aden, da Tekun Indiya, da kuma tekun Mediterrenean, kuma ta yi barna ga jiragen ruwa sama da 80, jiragen ruwa biyu sun nutse da kuma wasu jiragen da kwace.

Dakarun kasar ta Yemen sun sha gargadin dukkanin kamfanonin da suke hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da cewa: Jiragen ruwansu zasu fuskanci hare-hare a lokacin da suke wucewa ta yankin da aka ayyana kakaba takukunmi kansu ba tare da la’akari da inda suka fito ba, suna mai jaddada cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan sojojin na Yemen. don cimma nasara taimakawa al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma jajircewarsu na gwarzonta har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri ka Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments