Iran Ta Bukaci Kungiyar BRICS Ta Kafa Kawancin Yaki Da Takunkuman Tattalin Arziki

Gwamnatin JMI ta bukaci kasashen kungiyar tattalin arziki ta BRICS su samar da kawance ta yaki da takunkuman tattalin arziki na zalunci wadanda kasashen yamma

Gwamnatin JMI ta bukaci kasashen kungiyar tattalin arziki ta BRICS su samar da kawance ta yaki da takunkuman tattalin arziki na zalunci wadanda kasashen yamma musamman Amurka suke dorawa kasashen masu yenci a duniya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ali Akbar Ahmadiyan babban sakataren majalisar tsaron ta koli ta kasar Iran yana fadar haka a taron manya-manayan jami’an tsaro na kungiyar raya tattalin arziki ta BRICS wanda ke gudana a halin yanzu a birnin St. Petersburg na kasar Rasha.

Ahmadiyyan ya karada  cewa kawancen yaki da takunkuman tattalin arziki zai samar da tsaro ga harkokin kasuwanci ga kasashen kungiyar da kuma sauran kasashen duniya.

Jami’in tsaron ya kara da cewa dole ne kasashen kungiyar BRICS da ‘Global south’ su samar da tsaro a bangarori daban daban, wadanda suka hada da, tsaro na tattalin arziki, tsaron a bangaren takunkuman tattalin arziki, tsaro na makamshi, tsaro a bangaren abinci, tsaro kan kudade, tsaro a ruwan tekuna, al-adu, da kuma tsaron duniya gaba daya.

Ahamadiyyar ya kammala da cewa, a wannan halin da duniya take ciki kuma take sauyawa akwai bukatar tabbatar da tsaro ta ko ina a duniya wanda zai maye girbin wanda kasashen yamma suka yi babakere a kansa, kuma babu abinda yake haifarwa sai karin tashe tashen hankula a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments