‘Yan Gwagwarmayar Lebanon Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

‘Yan gwagwarmayar Lebanon suna ci gaba da kai hare-hare kan wurare da tarukan sojojin yahudawan sahayoniyya makiya ‘yan mamaya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da

‘Yan gwagwarmayar Lebanon suna ci gaba da kai hare-hare kan wurare da tarukan sojojin yahudawan sahayoniyya makiya ‘yan mamaya

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ke kasar Lebanon tana ci gaba da kai farmaki kan wuraren da aka jibge sojojin makiya ‘yan mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a kan iyakar Lebanon da Falasdinu, don nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu da suke ci gaba da tsayin daka a Zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayar kare kai mai daraja da kima gami da jajurcewar neman ‘yanci, da kuma mayar da martani ga ‘yan sahayoniyya masu kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummun Lebanon.

A halin da ake ciki dai, da misalin karfe 01:00 na safiyar yau alhamis ne ‘yan gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi suka kai wasu jerin farmaki kan Bayadh Balida da manyan bindigogi tare da tarwatsa wurin kai tsaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments