Mujallar “Newsweek” ta Amurka ta yi magana kan fifikon kasar Sin kan Amurka a nahiyar Afirka, ta hanyar sauya salon zuba jari da tsare-tsare a wannan nahiya.
Mujallar “Newsweek” ta kasar Amurka, ta yi tsokaci a cikin wani rahoto, kan tsarin da kasar Sin ta bi a baya-bayan nan kan dangantakarta da kasashen nahiyar Afirka, inda ta jaddada cewa, ta fi Amurka a wannan yanki.
Mujallar ta bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin samar da tallafin dala biliyan 51 ga kasashen Afirka, yayin taron koli karo na 9 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, a lokacin da yake karbar bakuncin shugabannin nahiyar a birnin Beijing a makon jiya, “a daidai lokacin da kasar Amurka ta ke yin hadin gwiwa da kasashen Afirka a kokarin dawo da tasirinta a yankin.”
Ta yi nuni da cewa, kasar Sin ta dauki nauyin wannan taron, wanda ake gudanarwa a duk bayan shekaru 3 tun daga shekarar 2000, yawancin kasashen Afirka 53 da suka aike da tawaga a taron, in ban da Swaziland – wadda ta kasance kasa daya tilo ta Afirka kasar da ke kula da huldar diflomasiyya da Taiwan maimakon kasar Sin.
Mujallar ta bayyana cewa, “A ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tana ba da gudummawar manyan ayyuka, kamar gadoji, da tituna, da tashoshin jiragen ruwa, wadanda akasari a kasashe masu tasowa ne, ciki har da Afirka, ta yadda wadannan hannayen jarin sun kasance wani muhimmin bangare na ci gaban da shugaban kasar Sin ya samu a duniya.
Yayin da kasashe da dama suka kasa biyan basussukan wadannan ayyuka, “China ta sake fasalinta tare da yin shawarwari kan rancen ta, musamman bayan yaduwar cutar numfashi ta Covid-19, wanda ya ta’azzara yanayin tattalin arziki a kasashe da dama,” a cewar mujallar, wanda hakan ya hada har ma da yin tunani yafe wa wasu kasashe basussukan, wasu China tana tunanin sassauta musu.