Ambaliyar Ruwa A Najeriya Ta Yi Mummunar Illa A Jihar Borno

Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Malam Barkindo Mohammed, ya bayyana cewar halin da ake ciki a Maiduguri sakamakon

Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Malam Barkindo Mohammed, ya bayyana cewar halin da ake ciki a Maiduguri sakamakon afkuwar ambaliyar ruwa ya munana.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito Dam ɗin Alau ne ya ɓalle da sanyin safiyar Talata, lamarin da ya sa ruwa ya mamaye yankuna da dama a garin.

Dubban mazauna garin sun rasa matsugunansu kuma suna neman wuraren da za su fake.

Mohammed, ya ce hukumar ta fara aikin ceto da kuma raba buhunan yashi don hana ruwan ya ƙara kwarara zuwa wasu yankuna.

“Muna kan aikin ceto yanzu haka, kuma mun raba buhunan yashi a Gozari. Yayin da nake magana da ku yanzu, ni da ma’aikatana mun maƙale; mun zo ceton wasu mutane amma yanzu muna cikin tsaka mai wuya,” in ji shi.

A halin yanzu, daruruwan mutane sun nemi mafaka a kan tituna ba tare da sanin inda za su je.

Wasu mazauna garin na zaune ko kwance ne a ƙarƙashin bishiyoyi tare da iyalansu.

Wani magidanci mai mata biyu da yara shida, Musa Abbas, ya ce ba shi da inda zai je.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments