Kungiyar Human Right Watch Ta Ce Na’urorin Binciken Isra’ila Suna Cutar Da Falasdinawa

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce: Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila tana amfani da na’urorin binciken neman bayanan sirri mai

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce: Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila tana amfani da na’urorin binciken neman bayanan sirri mai zurfi a yakin Gaza

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce, amfani da na’urorin fasahar sa ido da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, da amfani da na’urorin binciken neman bayanan sirri da kuma sauran kayan aikin dijital don neman gano wuraren da ake kaddamar da hare-haren da ake kai wa daga Gaza na kara hadarin yiwuwar cutar da fararen hula, sannan wadannan kayan aikin na zamani suna haifar da matsaloli masu girma a fagen rayuwa, doka, harkokin jin kai da sauransu.

Kungiyar ta kara da cewa a cikin wata takarda ta tambaya da amsa da aka fitar a ranar Talatar da ta gabata cewa: Wadannan kayan aikin na dijital a wasu lokuta suna dogara ne a kan bayanan karya da kuma kirdadon da ba su da tabbas don samar da ayyukan soji da bayanai ta hanyoyin da suka ci karo da manufofin haramtacciyar kasar Isra’ila wadanda a karkashin doka suka sabawa matakan jin kai na kasa da kasa, musamman ka’idojin kiwon lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments