Amurka Ta Gargadi Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Shiga Yaki Da Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon

Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila Haaretzta watsa labarin cewa: Amurka ta gargadi haramtacciyar kasar Isra’ila game da kunna yakin basasa da Lebanon Jaridar yahudawan sahayoniyya ta

Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila Haaretzta watsa labarin cewa: Amurka ta gargadi haramtacciyar kasar Isra’ila game da kunna yakin basasa da Lebanon

Jaridar yahudawan sahayoniyya ta Haaretz ta nakalto daga wani jami’in Amurka da ke da masaniya kan kyakkyawar alakar Amurka da haramtaciyar kasar Isra’ila yana cewa: Gwamnatin Amurka ta gargadi haramtacciyar kasar Isra’ila game da kaddamar da yakin basasa da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.

Jami’in ya yi nuni da cewa: Gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden tana goyon bayan matakan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take dauka kan kungiyar Hizbullah, amma ya yi imanin cewa, dole ne a yi la’akari da sakamakon yakin da ake yi da Lebanon.

Ya jaddada cewa, Amurka ta bayyana fargabarta kan sake yiwuwar wargajewar yarjejeniya tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, a hali yahudawan sahayoniyya suna tunanin shiga yaki da kungiyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments