Gaza: Asbitoci Guda Biyu A Gaza Suna Dab Da Dakatar Da Aiki Saboda Karancin Makamashin Bada Wutan Lantarki

Asbitoci guda biyu a gaza suna dab da dakatar da ayyukan ceton rayuwan falasdinawa saboda karewar makamashi a injunan bada wutan lantarki na su. Kamfanin

Asbitoci guda biyu a gaza suna dab da dakatar da ayyukan ceton rayuwan falasdinawa saboda karewar makamashi a injunan bada wutan lantarki na su.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Asbitin Kamal Adwan da kuma Asbitin Indonsia dukansu a garin Beit Lahia sun kusan rufewa saboda karancin makamashi mai bada wutan lantarki.

Gwamnatin HKI dai tun bayan fara yakin Tufanul Aksa watanni 11 da suka gabata ta hana shigo da makamashi abicni da kuma dukkanin abin bukatu na rayuwar mutanen a gaza. Kari a kan kisan Falasdinawa da take yi da raunata wasunsu a duk ranar All..

Dr Hussam Abu Safia daraktan asbitin Kamal Adwan ya fadawa tashar talabijin ta Aljazeera na kasar Qatar kan cewa Asbitansa zai dakatar da dukkan ayyuka na ceton ran falasdinawa nan da sa’o’i 48, idan ba’a samo masa makamashin a injunan bada wutan lantarki na asbitinsa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments