Kanani: Fitar Da Rai Daga Samun Nasara Ne Yasa Isra’ila Kona Yankunan Falastinawa

Parstoday – Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, janyewar sojojin Isra’ila daga sansanin Jenin da kuma birnin Tulkarm da haramtacciyar kasar Isra’ila

Parstoday – Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, janyewar sojojin Isra’ila daga sansanin Jenin da kuma birnin Tulkarm da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi daga wasu yankunan Jenin da kuma kone su, sakamako ne na gaza samun nasarar da take bukata a kan al’ummar falastinu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanani ya rubuta a dandalin  X cewa: rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan shafe kwanaki 10 ana kai hare-hare kan sansanin Jenin da kwanaki 4 na mamaye birnin Tulkarm da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan, Gwamnatin Isra’ila ta ja da baya daga wadannan garuruwa biyu.

A rahoton Parstoday, Kanani ya kara da cewa: Hotunan yadda Isra’ila take lalata dukkan gine-ginen birane, da abubuwan more rayuwa da na hidima a yankin zirin Gaza,  da kuma wasu sassan arewacin gabar yammacin kogin Jordan, musamman ma “Jenin” da “Tulkarm”  hakan ya nuna cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kasa cimma burinta, sakamakon tsayin daka da al’ummar Palasdinu suke yi a gaban ‘yan mamaya.

Kanani ya kara da cewa: Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suna da alhakin day a rataya a kansu, na tabbatar da cewa an zayyana wadannan lafuka na Isra’ila a cikin laifukan yaki da ake zarginta da aikatawa a gaban kotun manyan laifuka ta duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments