Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jinjinawa Kasar Yemen Kan Goyon Bayanta Ga Falasdinawa

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yaba da matsayin da wannan kasa ta Larabawa Yemen take takawa kan laifukan ‘yan mamaya Ministan harkokin wajen kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yaba da matsayin da wannan kasa ta Larabawa Yemen take takawa kan laifukan ‘yan mamaya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yaba da matsayin gwamnati da al’ummar kasar Yemen dangane da kalubalantar muggan laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan Zirin Gaza a daidai lokacin da kasashe da dama suka takaita da furta kalaman suka da tofin Allah tsine kan zaluncin yahudawan sahayoniyya kawai.

Yayin wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da ministan harkokin wajen gwamnatin ceto kasa ta Yemen Jamal Amir, Araqchi ya ce dangantakar da ke tsakanin Iran da Yemen da kuma ci gaba da tuntubar juna a tsakanin bangarorin biyu da nufin inganta tsaron yankin yana da matukar muhimmanci.

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa matsayin gwamnati da al’ummar kasar Yemen dangane da kalubalantar ayyukan laifukan yaki da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Zirin Gaza, inda ya ce: A daidai lokacin da kasashe da dama suka takaita da bayyana matsayarsu ta yin Allah wadai kan ayyukan ta’addancin ‘yan sahayoniyya kawai, gwamnatin Yemen da al’ummar Yemen a fili sun fito suna kalubalantar ayyukan zaluncin yahudawan sahayoniyya kan Falasdinawa.

Araqchi ya gayyaci ministan harkokin wajen kasar Yemen da ya ziyarci birninh Tehran fadar mulkin kasar Iran domin ci gaba da tattaunawa da musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi moriyar kasashen biyu da na yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments