Babban Malamin Musulunci A Moroko Ya Yabawa ‘Yan Shi’a Kan Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu

Wani shararren malamin addinin Musulunci a kasar Moroko ya bayyana cewa: ‘Yan Shi’a sun fi ‘yan Sunni karfin gwiwar tallafa wa Falasdinawa Shararren malamin addinin

Wani shararren malamin addinin Musulunci a kasar Moroko ya bayyana cewa: ‘Yan Shi’a sun fi ‘yan Sunni karfin gwiwar tallafa wa Falasdinawa

Shararren malamin addinin Musulunci kuma masanin ilimin fikihu a kasar Moroko, Dr. Ahmed Raissouni, ya jaddada cewa: ‘Yan Shi’a Mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah sun bayar da goyon baya na mai girma ga gwagwarmayar Falasdinawa, yana mai cewa wannan tallafin yana kunshe ne a cikin samar da rayuka, kudade, makamai, da kuma sadaukarwa mai girma, wanda Dr Raissouni ya bayyana a matsayin wani abu mai kima da ‘yan Ahlus-Sunna waj-Jama’a ba su aikata ba ga ‘yan uwansu da suke bukatar ire-iren wadannan tallafi.

Wadannan bayanai sun zo ne a cikin kasidarsa mai taken “Ku kuma tsayar da shaida saboda Allah,” inda Al-Raissouni ya yi nuni da cewa abin da ya ce tabbatar da gaskiya ce da tsayar da adalci, yana mai jaddada cewa bayyana wannan shaidar wani wajabci ne na shari’a na fuskantar yakin masu kokwanton goyon bayan ‘yan shi’a ga al’ummar Falastinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments