An yi gagarumar zanga-zanga a birnin Landan domin yin kira da a tsagaita wuta a Gaza

Dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan tituna a birnin Landan na kasar Birtaniya domin yin kira da a gaggauta tsagaita bude wuta a zirin

Dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan tituna a birnin Landan na kasar Birtaniya domin yin kira da a gaggauta tsagaita bude wuta a zirin Gaza tare da neman a dakatar da baiwa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila makamai gaba daya a yakin da take yi na kisan kare dangi a yankin.

Masu zanga-zangar sun taru ne a Piccadilly Circus da ke tsakiyar birnin Landan a ranar Asabar, inda daga bisani suka yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Isra’ila, yayin da suke dauke da tutocin Falasdinawa da rera taken nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu.

Mahalarta zanga-zangar sun kuma bukaci gwamnatin Birtaniya da ta kara kaimi wajen ganin ta dakile kashe-kashen da ake ci gaba da yi a Gaza, wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40,000 cikin watanni 11 da suka gabata.

Zanga-zangar ta baya-bayan nan dai ta zo ne bayan da gwamnatin Birtaniya ta sanar da matakin da ta dauka na haramta bayar da makamai ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta ce wani bangare na haramcin zai dakatar da lasisin fitar da makamai kashi 30 na kamfanonin kera makaman da ke baiwa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kayan aikin soja.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ne ya sanar da matakin a ranar Litinin din da ta gabata a daidai lokacin da ake sukar yadda Burtaniya  ke da hannu a kisan gillar da ake yi a Gaza, wanda hakan ya sabawa wa dokar jin kai ta duniya.

Dakatarwar ta biyo bayan zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa na tsawon watanni a birnin Landan da wasu biranen kasar Burtaniya, na neman a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza da kuma dakatar da sayar da makamai da Birtaniyya ke yi wa Isra’ila.

Tun lokacin da Isra’ila ta fara yakin kisan kare dangi a Gaza a farkon watan Oktoban shekarar da ta gabata, Birtaniya, da ma Amurka, ke baiwa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila dukkanin makamai da alburusai da take yin amfani da su wajen kisan fararen hula mata da kananan yara a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments