A Yau Ne Ake Zaben Shugaban Kasa A Kasar Aljeriya

A yau Asabar 7 ga watan Satumba ne ake saran mutanen kasar Aljeriya kimani miliyon 24.3 zasu fito zuwa rumfunan zabe don zaben shugaban kasa

A yau Asabar 7 ga watan Satumba ne ake saran mutanen kasar Aljeriya kimani miliyon 24.3 zasu fito zuwa rumfunan zabe don zaben shugaban kasa daga cikin yan takara uku da suka fito don hakan.

Shafin yanar gizo na labarai Africa-News ya bayyana cewa yan takaran guda uku, sun kammala yakin neman zabe na makonni uku a duk fadin kasar kuma batun kyautata rayuwar mutanen kasar musamman a bangaren tattalin arziki na daga cikin al-amuran da suka yi ta yakin neman zabe da shi. Sai kuma yaki da cin hanci da rashwa da kuma wasu attajiran kasar da suke wawaso da dukiyar kasar.

Shugaba mai ci Abdelmadjid Tebboune yana samun goyin bayan wasu manya manyan jam’iyyu a kasar duk da cewa shi dan takarar indipenda ne. Sai kuma  Youcef Aouchiche na jam’iyyar gurguzu da kuma Abdelaâli Hassani Cherif na jam’iyyar MSP.

Masana suna ganin shugaba Tebbouune yana iya lashe zaben, wanda kuma zai bashi damar shugabancin kasar na wasu shekaru 5.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments