Jakadan Iran A M.D.D Ya Yi Watsi Da Zargin Cewa: Kasarsa Tana Taimakon Rasha Da Makamai   

Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya yi tsokaci kan zargin cewa; Kasarsa tana aika makamai masu linzami zuwa Rasha Dangane da rahotannin da suke

Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya yi tsokaci kan zargin cewa; Kasarsa tana aika makamai masu linzami zuwa Rasha

Dangane da rahotannin da suke zargin cewa: Iran tana aikewa da makamai masu linzami zuwa kasar Rasha, wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya sanar da cewa, matsayar Iran kan rikicin Ukraine bai canza ba.

Wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, a yammacin jiya Juma’a, yayin da yake amsa tambayoyi game da rahotannin da suke zargin Iran da aikewa da makamai masu linzami zuwa kasar Rasha: Yana mai jaddada cewa: Matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da rikicin kasar Ukraine bai canja ba, saboda Iran tana daukan aikewa da taimakon soji ga bangarorin biyu da ke rikici da juna, wanda ke haddasa hasarar bil’adama da na ababen more rayuwa, tare da ficewa daga tattaunawar tsagaita bude wuta, a matsayin rashin mutuntaka, saboda da haka, ba wai kawai ta yi watsi da zarge-zargen ba ne, har ma tana yin kira ga sauran kasashe da su daina aika makamai ga bangarorin biyu da ke rikici.

A baya dai jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da zarge-zargen “marasa tushe da asali da suke matsayin makirci da yaudarar Amurka, Birtaniya da Faransa da suke kitsawa kan kasar Iran da nufin rusa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da Ukraine, yana mai cewa: Amurka da kawayenta ba za su iya boye gaskiyar da ba za a iya musantawa ba na yadda kasashen yammaci suke ci gaba da tura muggan makamai ga Ukraine musamman daga Amurka da nufin ganin sun tsawaita yakin Ukraine tare da cutar da fararen hula da kayayyakin more rayuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments