Limamin Tehran Ya Ce: Turawa Suna Ba Da Lambar Yabo Ga Masu Kisan Kiyashi Kan Fararen Hula

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Turawan Yamma suna ba da lambar yabo ta zaman lafiya ga masu zubar

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Turawan Yamma suna ba da lambar yabo ta zaman lafiya ga masu zubar da jinin bil’Adama

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, Ayatullah Sayyid Ahmed Khatami, ya ce an riga an zartar da mummunan hukunci ga masu aikata muggan laifuka da zubar da jinin bil’Adama, amma har yanzu Turawan Yamma suna ba da lambar girma da yabo ta zaman lafiya ga wadanda dabi’arsu ta kasance zubar da jinin bil’Adama da aikata muggan laifuka.

Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya tabo batun zagayowar shekarar da karnukan farautar tsohuwar masarautar Pahlawi suka shekar da jinin al’ummar Iran masu dauke da ruhin juyin juya halin Musulunci masu tarin yawa a ranar Juma’ar Jini, a ranar 17 ga watan Shahrivar da ta yi daidai da ranar 8 ga watan Satumban shekara ta 1978 a dandalin shahidai na birnin Tehran fadar mulkin kasar, inda ya bayyana cewa, al’umma sun ga wannan bakar zaluncin, sannan sun ga yadda aka kawo karshen wannan azzalumar gwamnati a ranar 22 ga watan Bahman na shekarar 1357 hijira shamsiyya wanda ya zo daidai da ranar 11 ga watan Fabrairun shekara ta 1979   

Sayyid Khatami ya kara da cewa: An kawo karshen wadannan masu aikata muggan laifuka da zubar da jini, amma har yanzu Turawan Yamma suna ba da lambar yabo ta zaman lafiya ga masu dauke da irin wadanda muggan dabi’u ta zubar da jini da aikata muggan laifuka.

Sannan Limamin ya tabo yadda yahudawan sahayoniyya suka kashe Falasdinawa da suka hada da mata da kananan yara da ba ji ba, ba su gani ba da suka haura 40,000 a Gaza, amma ba a daukansu a matsayi masu laifi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments