Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Ta Goyon Bayan ‘yan Gwagwarmaya

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Suna ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar Falasdinawa da dukkan karfinsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa:

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Suna ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar Falasdinawa da dukkan karfinsu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Gwamnatinsa a shirye take ta ci gaba da ba da cikakkiyar kariya ga gwagwarmayar dukkanin al’ummar da ake zalunta a duniya kan ma’abota girman kai, musamman gwagwarmayar al’ummar Falastinu da ake zalunta a fagen kalubalantar yahudawan sahayoniyya.

Wannan dai ya zo ne a cikin sakon da shugaba Pezeshkian ya aike wa taron kasa da kasa mai taken “Mujahidai a gudun hijira,” wanda aka fara gudanar da zamansa na tara da hukumar lardin Semnan da ke gabashin kasar Iran ta shirya a jiya Talata, tare da karbar bakwancin baki daga kasashen musulmi daban-daban tare da jami’an Iran masu yawa.

Shugaban ya tuna tsohon shugaban Iran Shahidi Ibrahim Ra’isi da ministan harkokin wajensa Hossein Amir Abdullahian, yana mai bayyana su a matsayin “Jami’an diflomasiya masu zurfin tunani wadanda suka gabatar da kyakkyawan misali a harkar diflomasiyya ingantacciya.

Pezeshkian ya kara da cewa: Tun bayan da ya hau kan karagar shugabanci a gwamnati ta 14, yake jaddada aniyarsa ta ci gaba da goyon bayan al’ummar Falastinu da kuma al’ummar duniya da ake zalunta, tare da cikakken shiri a dukkanin bangarori na kwato musu hakkokinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments