Rikicin Jami’an Libiya Ya Janyo Tabarbarewar Al’amura A Kasar Tare Da Rashin Biyan Albashi

Rikicin babban bankin kasar Libiya ya janyo tsaiko wajen biyan albashi tare da kara haifar da wahalhalun ga al’ummar kasar Rahotonni daga Libiya suna nuni

Rikicin babban bankin kasar Libiya ya janyo tsaiko wajen biyan albashi tare da kara haifar da wahalhalun ga al’ummar kasar

Rahotonni daga Libiya suna nuni da cewa: A bankuna da shagunan kasuwanci da kuma kamfanoni a duk fadin kasar Libiya, suna nuna yadda ake ciki na yanayin rudani, tsoro da kuma durkushewar hada-hadar kasuwanci, tun bayan bullar rikici tsakanin bangarorin da ke mulkin kasar da kuma fafutukar karbe iko da babban bankin kasar ta Libya, lamarin da masu sharhi ke ganin kan iya kara muni.

Al’ummar Libiya da kamfanin dillancin labaran reuters ya tuntuba sun  bayyana cewa: Suna fatan idan Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taro da shugabannin siyasar kasar masu adawa da juna, za a yi nasarar shawo kan rikicin, inda a halin yanzu yawancin hada-hadar da aka saba yi ba za su yiwu ba, kuma an jinkirta biyan albashi ga ma’aikatan kasar da dama.

Rikicin dai ya fara ne a lokacin da shugaban majalisar gudanar da shugabancin kasar Mohamed Al-Manfi ya sanar da korar tsohon gwamnan babban bankin kasar Al-Siddiq Al-Kabir tare da nada sabon kwamitin gudanarwa, matakin da ya takaita ga hukumomin majalisar kasar kawai a karkashin dokokin da ke gudana a kasar a halin yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments