Dakaru Masu Gwagwarmaya A Iraki Sun Cilla Makaman ‘Drons’ Kan Tashar Jiragen Ruwa Ta Haifa A HKI

Dakaru masu gwagwarmaya da yan ta’adda a kasar Iraki sun bada sanarwan amfani da makaman ‘Drone’ don lalata wasu wurare masu muhimmanci a birnin Haifa

Dakaru masu gwagwarmaya da yan ta’adda a kasar Iraki sun bada sanarwan amfani da makaman ‘Drone’ don lalata wasu wurare masu muhimmanci a birnin Haifa na HKI a jiya da dadare.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dakarun na fadar haka a safiyar yau larabawa a wata sanarwan da suka fitar.

Labarin ya kara da cewa, makaman drones samfurin ‘kamikaze’  sun fada a wani wuri mai muhimmanci a birnin Haifa na HKI ya kuma lalata shi.

Labarin ya kara da cewa dakarun na Iraki sun yi haka ne don tallafawa Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke kashewa a Gaza tun watanni kimani 11 da suka gabata.

Har’ila yau dakarun na Iraki sun sha alwashin ci gaba da irin wadan nan hare hare matukar gwamnatin HKI ta ci gaba da ya ki a gaza, inda take kashe mata da yara.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne sojojin HKI suka fara luguden wuta a Gaza, bayan da kungiyar Hamas ta kutsa cikin matsugunan yahudawa a kusa da Gaza suka kashe sojojin yahudawa suka kuma kama wasu suka shigo da su Gaza.

Falasdinawa 40,819 ne suka yi shahada tun lokacin, sannan wasu 94,291 ne suka ji rauni. Banda haka wasu miliyon 1.7 sun zama yan gudun hijira saboda an rusa gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments