Kafafen yada labarai na HKI sun bada sanarwan cewa gwamnatin HKI ta tsawaita aikin sojen da ta ke yi a yankin yamma da kogin Jordan musamman a birnin Jenin bayan da ta gamu da turjiya mai tsanani daga dakarun falasdinawa masu gwagwarmaya a yankin.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa a jiya Talata ce yakamata sojojin yahudawan su kawo aikin aikin soje na musamman da suka fara a yankin yamma da kogin Jordan.
Labarin ya kara da cewa, yau kwanaki 8 kenan da fara aikin soje na musamman a wasu garuruwa a arewacin yankin yamma da kogin Jordan sai dai sojojin yahudawan sun kasa samun iko da wasu yankuna wadanda mayaka falasdinawa a Jenin suke iko da shi.
Wasu majiyoyin sun kara da cewa gwamnatin Natanyahu, a dole ta janye wasu sojojinta daga Gaza zuwa yankin yamma da kogin Jordan don murkushe falasdinawa a yankin.