Kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen saman yakin Ukraine marasa matuka ciki guda 158 a wasu munanan hare-haren da aka kai mata cikin daren jiya
A safiyar yau Lahadin nan ne kasar Rasha ta sanar da dakile wasu sabbin hare-haren jiragen sama marasa matuka, wadanda suka hada da wani “babban hari” a yankin Bryansk dake daura da kan iyaka da Ukraine, da kuma wani harin da aka kai kan babban birnin kasar Rasha, ba tare da an samu asarar rai ba.
Na’urorin tsaron saman Rasha sun yi nasarar kakkabo jiragen saman yaki marasa matuka ciki da Ukraine ta harba guda 158 a kan yankuna 15 na Rasha a cikin daren jiya, ciki har da biyu a kan babban birnin kasar, Moscow, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar a yau Lahadi. Ma’aikatar ta bayyana a cikin shafinta na Telegram cewa mafi yawan jirage marasa matuka ciki guda 122, an harbo su ne a yankunan Kursk, Bryansk, Voronezh da Belgorod da ke kan iyaka da Ukraine.
Gwamnan yankin Alexander Bogomaz ya ce da misalin karfe (22:00 na agogon GMTne) na ranar Asabar ce na’urarar kariyar sararin samaniyar Rasha suka dakile wani yunkurin kai hari da jiragen sama marasa matuka ciki a yankin na Bryansk. Yana fayyace cewa sojojin Rasha sun gano aƙalla jirage marasa matuki 26 tare da lalata su, ba tare da haifar da rauni ko lalata wani abu ba.