Iran ta yi kira da a dauki mataki mai tsauri a duniya don dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi

Babban daraktan kula da ayyukan zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce, mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar

Babban daraktan kula da ayyukan zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce, mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ita ce babban abin da ke kawo cikas ga samun daidaito da ci gaba mai dorewa a kasashen musulmi da yankin gabas ta tsakiya.

Asadullah Eshraq Jahromi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC karo na 50 a birnin Yaounde na kasar Kamaru ranar jiya Juma’a.

Eshraq Jahromi ya bayyana matukar damuwarsa kan irin ta’asar da Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa da ake zalunta a yankin Zirin Gaza tsawon watanni goma sha daya da suka gabata, tare da yin tir da kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyah a ranar 31 ga watan Yuli a Tehran.

Ya yi kira ga kasashen duniya da kuma na OIC, da su dauki wani muhimmin mataki da nufin dakatar da ayyukan Isra’ila cikin gaggawa, wadanda suka hada da laifukan yaki, cin zarafin bil’adama da kuma kisan kare dangi.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada wajabcin dorawa Isra’ila alhakin laifukan da take aikatawa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da ma sauran yankunan yankin.

Eshraq Jahromi ya jaddada cewa, dole ne a magance matsalolin rashin tsaro da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments