ِ Dantakarar Shugabancin Kasar Iran Zakani Ya Ce; Abinda Kawai Muke Bukata  A Fagen Nukiliya Shi Ne Hakkokinmu

Dan takarar shugabancin kasar ta Iran Ali Riza Zakani wanda tashar talabijin din ‘al’alama’ mai watsa shirinta da larabci daga nan Iran ta yi hira

Dan takarar shugabancin kasar ta Iran Ali Riza Zakani wanda tashar talabijin din ‘al’alama’ mai watsa shirinta da larabci daga nan Iran ta yi hira da shi, ya ce: Idan ya zama shugaban kasa,zai gudanar da ayyuka na kare mutunci, kuma cikin hikima domin kare maslahar kasa.

Zakani wanda yake Magana akan alaka da kasashen makwabta kamar su Iraki da Saudiyya ya kuma ce; Ba zai zama bakon abu ne makwabtan namu ya zamana suna da nasu manufofin da su ka fi bai wa muhimmanci a daura da namu abubuwan da mu ka bai wa muhimmanci a karkashin kawancen gwagwarmaya.

Har ila yau Zakani ya ce, Iran za ta bayar da muhimmanci ga manyan kasashen da suke a cikin wannan yankin na Asiya kamar Cina da kuma Rasha da za mu cigaba da yin aiki mai karfi a tare da su.

Hari la yau, dan takarar shugabancin kasar ta Iran ya kuma yi ishara da wasu kasashen da za a a bai wa muhimmanci wajen kulla alaka da su, da sun hada India, Brazil da kuma Afirka Ta Kudu, sai kuma sauran kasashen da suke girmama Iran, in ban da HKI da Amurka wacce babu wani sauyi dangane da matsayarta akan Iran.

Dangane da shirin Iran na makamashin Nukiliya na zaman lafiya, Zakani ya ce; Cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya wani hakki ne na dabi’a ga dukkanin kasashe da su ka hada da Iran. Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Iran din take aiki da dukkanin dokokin hana yaduwar makaman Nukiliya,don haka ba wani abu take nema ba wanda ya wuce hakkokinta na dabi’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments