An fara taron na Francophonie na kasashe masu amfani da harshen Faransanci ne, wanda kasar Cambodia ta soma karbar bakuncinsa a jiya Lahadi. Sai dai taron na gudana ne a daidai lokacin da Baraka tsakanin muhimman manbobin kungiyar ke barazanar sanyawa daya da cikinsu ficewa daga cikinta.
Ƙalubalen da taron na kwanaki ke fuskanta dai shi ne tsamin dangantakar shugaban Jamhuriyar Congo Felix Tshisekedi, da takwaransa na Rwanda Paul Kagame, waɗanda baya ga batun ‘yan tawayen M23, suke takaddama kan wanda zai cigaba da jagorancin kungiyar ta Francophonie.
Ficewar Congo daga Francophonie dai zai zama babban koma baya ga ƙungiyar, la’akari da cewa Congon ce kasa ta biyu mafi yawan mutanen da adadinsu ya kai miliyan 57 masu amfani da harshen Faransanci bayan ita kanta Faransar.
A shekarar da ta gabata kungiyar ta Francophonie da ta kunshi kasashe da yankuna kusan 90, ta rasa manbobinta da suka hada da Nijar da Mali, da kuma Burkina Faso bayan kwace mulki da sojoji suka yi.