Leadership–Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta kara bai wa Nijeriya rancen wasu kudade da kuma zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa a kasar.
Tuggar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da gidan Talabijin na Channels a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya kara da cewa, Nijeriya ba ta cikin kasashen da ke fama da bashin da ya yi katutu, don haka, ba ta tattauna batun yafe basussuka da kasar Sin ba.