China ta bukaci kasar Amurka da ta dage duk wani takunkumi da ta kakaba kan kasar Iran da baya kan doka da ka’ida
2021-04-07 14:36:16

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Zhao Li Jiyan ya bayyana cewa: Dole ne a kan kasar Amurka ta koma cikin yarjejeniyar nukiliya da duniya ta cimma da kasar Iran, ba tare da gindiya wani sharadi ba gami da dage duk wani takunkumi da ta kakaba kan kasar ta Iran.
A zaman taron manema labarai da ya gudanar
a jiya Talata Zhao Li Jiyan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China ya yi
furuci da cewa: Kasar China tana goyon bayan kwamitin hadin gwiwa domin
tattauna batun dage duk wani takunkumi da Amurka ta kakaba kan kasar Iran tare
da kwadaitar da Iran kan yin aiki da dukkanin yarjeniyoyin da ta jinginar da su
a baya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen
kasar China ya fayyace cewa: Matakin bangare guda da tsohuwar gwamnatin Amurka
ta Donald Trump ta dauka na ficewa daga cikin yarjejeniyar da duniya ta cimma
da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukiliya shi ya janyo duk wannan
dambaruwar siyasar a halin yanzu.
Tags:
china ta bukaci kasar amurka
zhao li
ma’aikatar harkokin wajen kasar china
mai magana da yawun ma’aikatar
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!