Gawakin Jakadan Italiya A Kongo Demokradiyya Da Mai Tsaronsa Sun Isa Birnin Roma

2021-02-24 08:49:07
Gawakin Jakadan Italiya A Kongo Demokradiyya Da Mai Tsaronsa Sun Isa Birnin Roma

A jiya talata ce jirgin soja dauke da gawakin jakadan kasar Italiya a kasar Congo DMC da mai tsaronsa suka isa birnin Roma babban birnin kasar ta Italiya, inda firai ministan kasar Mario Draghi ya hadu da iyalan mamatan.

Jakada Luca Attanasio, dan shekara 43 a duniya da kuma mai tsaronsa Vittorio Iacovacci, dan shekara 30 a duniya sun hadu da ajalinsu ne a lokacinda suke kan hanyarsu ta duba wata makaranta wacce hukumar abinci ta duniya take ciyarwa ne sai suka hanu da wasu ‘yan bindiga 6, wadanda suka kashe direbansu, Mustafa Milambo sannan suka shiga da su dagi, amma a lokacin musayar wuta da jami’an tsaron kasar sai yan ta’adan suka kashe su.

Ministan cikin gida na kasar Congo ya na tuhumar kungiyat yan tawayen Rwandan na kabilar Hutu mai suna ‘Democratic Forces for the Liberation of Rwanda (FDLR)’ da kashe jami’in diblomasiyyan. Amma kungiyar ta musanta haka.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!