An Kashe Jakadan Kasar Italiya A Kasar Demokradiyyar Congo

2021-02-23 08:15:41
An Kashe Jakadan Kasar Italiya A Kasar Demokradiyyar Congo

A wani hari da aka kai wa tawagar hukumar Abinci dake karkashin MDD, an kashe jakadan na Italiya, mai gadinsa da kuma wani matuki da ke aiki da MDD a gabashin kasar a jiya Litinin.

Wadanda su ka rasa rayukan nasu su ne;Jakadan na Italiya Luca Attanasio dan shekaru 43, da jami’in tsaro Vittorio Lcovacci, mai shekaru 30, sai kuma matukun motar hukumar abinci ta duniya da ba a ambata sunansa ba.

Maharan da su ka bude wuta sun ji wa jakadan raununa da kuma sauran mutanen da suke tare da shi, sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar fitar da shi zuwa asibitin garin Goma.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin a yankin da yake kunshe da kungiyoyi masu dauke da makamai.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!