​Somaliya:An Ji Karar Tashin Bindigogi A Birnin Magadishu A Lokacinda Jam’iyyun Adawa Suka Fara Zanga-Zanga

2021-02-20 09:40:03
​Somaliya:An Ji Karar Tashin Bindigogi A Birnin Magadishu A Lokacinda Jam’iyyun Adawa Suka Fara Zanga-Zanga

An ji karar tashin bindigogi da karar fashewar nakiyoyi a wurare daban-daban a birnin Magadisho babban birnin kasar Somaliya a jiya Jumma. Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa jam’iyyun siyasar kasar Somaliya wadanda suke samun kariya daga mayakan sa kai, sun gudanar da zanga-zanga da ga babban titin da ta taso daga babbar tashar jiragen sama ta kasar.

Labarin ya kara da cewa sojojin gwamnati wadanda ake kira Gorgor sun bude wuta a kan masu zanga zangar wadanda suka hada da tsoffin jami’an gwamnatin kasar da kuma manya- manyan ‘yan siyasar.

Wani wanda ya ganewa idanunsa ya fadawa AFP cewa a cikin masu zanga zangar akwai tsohon firai ministan kasar Hassan Ali Kheire, da kuma tsohon shugaban kasar Sharif Sheikh Ahmed.

Kafin haka Sharif Sheikh Ahmed ya ce sojojin gwamnatin sun kai masu hari a hotel da suke zama a birnin da niyyar kashesu. Ya kuma kara da cewa sun bukaci mutane su fito zanga-zangar don kawo karshen shugabancin shugaba Farmaajoo wanda wa’adin shugabancinsa ya cika.

A ranar 8 ga watan Fabrayrun da muke cike ne yakamata a gudanar da zaben shugaban kasa kamar yadda ‘yan siyasa da kuma gwamnatin kasar, amm shugaban Mohammad Farmajoo ya kasa yin haka.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!