Ana Ci Gaba Da Samun Bayanai Akan Yadda Aka Sace Daliban Makarantar Kwana A Jihar Niger Da Ke Nigeria

2021-02-18 21:55:25
Ana Ci Gaba Da Samun Bayanai Akan Yadda Aka Sace Daliban Makarantar Kwana A Jihar Niger Da Ke Nigeria

Wani mazaunin daura da makarantar da aka sace yaran ya shaida wa manema labaru cewa; Maharan sun hada yara bibiyu su ka yi musu daurin gwami kafin su yi awon gaba da su.

Daliban kwalejin kimiyya ta gwamnati a garin Kagara da aka sace, su n kai 27, sai kuma ma’aikatan makarantar su 15.

Shaidar ganin idon ya fadawa jaridar Punch ta Nigeria cewa, da misalin karfe 2;00 na tsakar dare ne maharani da su ke sanye da kakin soja su ka kutsa cikin makarantar a juya Larabawa.

Wata majiyar ta shaida wa jaridar cewa; Daya daga cikin daliban mai suna Bejamin Abila ya gamu da ajalinsa a hannun maharani a yayin da ya yi kokarin daga murya domin akawo musu dauki.

Tuni dai gwmanan jihar ta Niger, Abubakar Sani Bello ya bayar da umarnin a rufe wasu makarantun kwana a cikin kananan hukumomi hudu saboda yadda garkuwar da mutane ya yawaita a yankunan.

Kananan hukumomin sun kunshi Rafi, Mariga, Munya da Shiroro.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!