Falasdin:Kunshin Alluran Riga Kafin Korona Na Farko Ya Isa Yankin Gaza

2021-02-17 22:06:30
Falasdin:Kunshin Alluran Riga Kafin Korona Na Farko Ya Isa Yankin Gaza

A yau Laraba ce ake saran kunshin alluran riga kafin cutar korona na farko zai isa zirin Gaza na kasar Falasdinu.Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto jami’an kiwon lafiya na yankin suna fadar haka, sun kuma kara da cewa idan sun isa alluran zasu isa yi wa mutane 1000 guda ne kacal a yankin, kuma zasu yiwa jami’an kiwon lafiya ne wadanda suke aiki dare da rana don yaki da cutar.

Kafin haka dai gwamnatin mamaya ta Isra’ila ta hana a shigo da alluran zirin na Gaza. Ya zuwa yanzu dai cutar korona ta kama mutane 53, 000 a yankin sannan 538 sun rasa rayukansu.

Fawzi Bargusi kakakin Hamsa ya ja kunnen Isra'ila kan hana shigowar alluran riga kafin cutar, samfurin Sputnik V ta kasar Rasha zuwa yankin. Ya kuma kara da yin hakan yana dai dai da take hakkin biladama sannan laifin yaki ne.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!