Kungiyar Wasan Volleyball Ta Mata Ta Korea Ta Kudu Ta Dakatar Da Yan Wasanta Biyu Kuma Tagwaye Don Nuna Fin Karfi

2021-02-15 21:23:37
Kungiyar Wasan Volleyball Ta Mata Ta Korea Ta Kudu Ta Dakatar Da Yan Wasanta Biyu Kuma Tagwaye Don Nuna Fin Karfi

Majiyar hukumar wasannin Volleyball ta kasar Korea ta kudu ta bada sanarwan dakatar da ‘yan wasa guda biyu mata, Lee Jae-yeong da ‘yar’uwarta Lee Da-yeong a yau Litinin saboda zargin nuna fin karfi da cin zali da suka yi a can baya.

Kamfanin dillancin labaran reuters daga Seoul babban birnin kasar Korea ta Kudu ya bayyana cewa tagwayen su na daga cikin wadanda aka zaba a wasannin Olympic wanda za’a gudanar a kasar Japan a wannan shekarar, amma wannan zargin ya sa aka dakatar da su daga wasannin.

Da farko dai wata tsohuwar abokiyar wasansu ce ta bayyana wannan zargin a makon da ya gabata a shafinta na twitter, kuma ta ce sun nuna mata fin karfi da cin zali ne tun suna makarantar sakandare.Yan wasan Volleyballa guda biyun dai, sun tabbatar da zargin kuma har sun nema afwar wadanda suke ci zalinsu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!