nukiliya : Martanin Zarif Ga Kasashen Turai Game Da Matakin Da Iran Ta Dauka

2021-02-13 14:48:50
nukiliya : Martanin Zarif Ga Kasashen Turai Game Da Matakin Da Iran Ta Dauka

Ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bukaci kasashen turai wadanda suka rage a yarjejeniyar nukiliyar kasar dasu karanci kudiri mai lamba 36 kwamitin tsaron MDD game da da yarjejeniyar ta 2015, da wasu wasiku da Iran ta aike kan wannan batun kafin su kai ga babatu game da matakan da Iran ke dauka a baya baya nan.

Zarif, ya maida maratani ga kasashen ne da suka hada da faransa, jamus, da kuma biritaniya, akan yadda suka kasa tabaka komai game da yarjejeniyar nukiliyar ta 2015.

Babu wani mataki da kasashen suka dauka na zahiri bayan ficewar Amurka daga yarjejniyar, amma su ne sahun gaba wajen kalubalentar duk wani mataki da Iran ita kuma take dauka.

Kawo yanzu dai a cewarsa babu wani abun azo a gani da kasshen turan suka tabaka ga ganin sun rage wa Iran, radadi game da takunkuman da Amurka ta lafta mata.

A cewarsa wannan ita ce kawai hanyar da Iran, zata nuna fishinta game da rashin cika alkawurin kasashen turawan uku bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar ta kuma ci gaba da lafta mata takunkumi.

Martanin na ministan harkokin wajen kasar ta Iran, na zuwa ne bayan da hukumar kula da makamashin nukiya ta duniya IAEA, ta sanar da cewa Iran ta soma samar da karfen uranium, duk da gargadin da kasashen Yammacin duniya suka yi mata cewa yin hakan tamkar keta yarjejeniyar makamin nukiliya ce da aka rattabawa hannu a 2015.

Iran dai ta ce tana yin hakan ne domin martani ga jerin takunkuman karya tattalin arzikin da gwamnatin Amurka karkashin jagoranci tsohon shugaba Donald Trump ta sanya mata a 2018 lokacin da ya yi watsi da jarjejeniyar da aka kulla.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!