​Isra'ila Na Ci Gaba Daukar Matakan Tsokanar Musulmi A Palestine

2021-02-13 09:12:48
​Isra'ila Na Ci Gaba Daukar Matakan Tsokanar Musulmi A Palestine

Yahudawa masu tsatsauran ra’ayi suna ci gaba da daukar matakan tsokanar musulmi a cikin birnin Quds.

Kafofin yada labarai na Palestine sun bayar da rahoton cewa, a ci gaba da daukar matakai na tsokana, a jiya Juma’a wasu yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai alfarma.

Rahotanin sun ce a cikin kasa da mako guda, daruruwan masu tsatsauran ra'ayi ne suka kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai afamar, da nufin tsokanar musulmi, yayin da kuma suke samun kariya daga jami’an tsaron Isra’ila.

Haka nan kuma a wani labarin, wasu yahudawan sun kai wani farmaki a kan yankunan musulmi a gabasin birnin Quds, tare da firgita mazauna yankin da tsoratar da su

Sannan kuma yahudawan sun sauya sunan yankin Jabir da ke gabashin birnin zuwa wani suna na yahudawa, da nufin tabbatar da mamayarsu a kanyankin da kuma gallaza wa musulmi.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!