​Najeriya: Rundunar Soji Ta Karyata Rahotanni Da Ke Cewa ‘Yan Boko Haram Sun Halaka Sojoji 20

2021-02-12 15:13:17
​Najeriya: Rundunar Soji Ta Karyata Rahotanni Da Ke Cewa ‘Yan Boko Haram Sun Halaka Sojoji 20

Rundunar sojin Najeriya ta karyata wasu rahotannin da suka nuna cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya har 20, a wata arangamar da su ka yi da jami’an tsaro na ‘Operation Lafiya Dole.

Daraktan Hulda Da Jama’a na Rundunar Sojojin Najeriya, Mohammed Yerima, ya bayyana cewa bayanin kisan da ake cewa an yi wa sojoji 20 ba gaskiya ba ne, a cewarsa an kirkiri labarin ne ba bisa dogaro da wasu dalilai ba.

A kan wannan rahoto ya ce, babu ma wani wuri da aka kaiwa rundunar soji hari a dukkanin wuraren da sojojin Najeriya suke yaki da mayakan kungiyar Boko Haram, harin baya-bayan nan da aka kai wa sojoji masu rakiya da kariya ga masu aikin titi kan hanyar Goniri zuwa Kafa, an yi shi ne tun a ranar 5 Ga wannan wata Fabrairu, sai kuma na Geidam a ranar 9 Ga Fabrairu, inda ya ce sojojin sun fatattakin maharani.

Wasu rahotanni da wasu kafofin yada labarai a najeriya suka bayar, sun nuna cewa mayakan kungiyar Boko haram sun yi wa sojojin Najeriya kwantan bauna acikin jihar Borno, inda suka kashe 20 daga cikin sojoji, tare da jikkata wasu.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!