Iran : Har Yanzu Amurka Ba Ta Nuna Da Gaske Ta Ke Ba_Ruhani

2021-02-11 20:57:55
Iran : Har Yanzu Amurka Ba Ta Nuna Da Gaske Ta Ke Ba_Ruhani

Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya bayyana cewa har yanzu sabuwar gwamnatin Amurka ba ta nuna da gaske ta ke yi ba, game da batutuwan da suka shafi Iran.

M. Ruhani, ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da wasu manyan ayyukan a ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa.

Shugaban kasar ta Iran, ya ce yanzu dai Iran, ta zura ido ta ga abunda sabuwar gwamnatin Amurkar za ta yi domin shafe laifufukan da tsohon shugaban kasar Donald Trump, ya aikata kan al’ummar Iran.

Har illa yau ya sake nanata cewa, siyasar matsin lambar da Amurka ta kwashe dogon lokaci tana yi Iran, ta cutura.

Don hake ne shugaba Ruhanin, ya bukaci sabuwar gwamnatin Amurka, data duba hanya mafi sauki domin tattaunawa da Iran ba wai amfani da matsin lamba ba, don kuwa duniya gabadaya ta shaida cewa matsin lamba kan Iran kam ya cutura.

Shugaba Ruhanin, ya bayyana Trump, da wanda ya shafe tsawon mulkinsa yana aikata ayyukan ta’addanci kan al’ummar Iran, da hana kasar samun magunguna a daidai lokacin da duniya ke fama da annobar korona.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!