Ministocin Afrika Sun Tattauna Game Da Tasirin Korona Kan Tattalin Arziki

2021-02-11 20:52:29
Ministocin Afrika Sun Tattauna Game Da Tasirin Korona Kan Tattalin Arziki

Ministocin kudi na kasashen nahiyar Afrika, sun tattauna da sakatare janar ta hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD Vera Songwe, da Manajan Daraktar Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF Kristalina Georgieva, dangane da gaggauta tunkarar tasirin annobar COVID-19 kan tattalin arziki.

Yayin taron da aka yi ta kafar bidiyo, dukkan ministocin sun yi kira da kara yawan kudaden ajiya na ketare da za a iya amfani da su a lokutan bukatar musamman, zuwa dalar Amurka biliyan 500.

Haka kuma ministocin sun bukaci da a kara samar da damar shiga kasuwanni da hanyar samun karin rance mai rangwame da tsawaita shirin biyan bashi, bisa la’akari da dogon lokaci da annobar ta ja.

Wata sanarwa da hukumar ECA ta fitar, ta ruwaito ministan kudin Ghana, Ken Ofori-Atta na cewa, sanin kowa ne za a ci gaba da fama da annobar nan da shekaru 2 zuwa 3, don haka me ya sa za a tsawaita lokacin biyan bashin da ake bin kasashen da watanni 6 maimakon maimakon shekaru biyu ?

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!