Kungiyar HRW Ta Zargi Sojojin Habasha Da Farmawa Fararen Hula
2021-02-11 20:50:13

Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa (Human Rights Watch) ta zargi gwamnatin Habasha da kai farmaki kan fararen hula da ababe masu fashewa.
A rahoton data fitar kungiyar ta ce sojojin na Habasha, sun jefa abubuwan fashewa a birane daban daban lokacin rikicin yankin Tigray, wanda kuma hakan a cewar HRW, sun saba wa dokokin yaki.
Rahoton ya ce an yi amfani da abubuwan fashewa a gidaje da makarantu da kasuwanni a hare-haren sojojin a yankin na Tigray, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 83 ciki har da yara kanana.
Ko baya ga hakan a cewar rahoton na HRW akwai mutane sama da dari uku da suka samu raunuka.
Babu dai wani martani daga gwamnatin ta Habasha kawo yanzu kan wannan rahoton, saidai a kwanakin baya fira ministan Habashar, Abiy Ahmed ya kare sojojin da zargin kashe fararen hula a yankin na Tigray.
024
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!