Dan Takarar Jami’iyyar PNDS-Tarayya Mai Mulki, A Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasa, Yana Bude Yakin Neman Zabe

2021-02-08 14:54:55
Dan Takarar Jami’iyyar PNDS-Tarayya Mai Mulki, A Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasa, Yana Bude Yakin Neman Zabe

Muhammad Bazum tare da jam’iyyun da suke mara masa baya a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a yi a nan gaba, ya shelanta da yakin neman zabe a birnin Niamey.

A yayin zabe zagaye na farko da aka yi a jamhuriyar ta Nijar, Muhammad Bazum ya sami kaso 39.30% na jumillar kuri’un da aka kada a ranar 27 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata.

A halin da ake ciki a yanzu dai Muhammadu Bazum din yana da goyon bayan jam’iyyun siyasa da su ka hada MNSD –Nasara, da MPR-Jamhuriya, RPP-Farilla da kuma ANDP-Zaman Lahiya.

An yi bikin kaddamar da yakin neman zaben ne dai a babban dakin taro na kasa da kasa na Mahatama Gandi da ke birnin Yamai, inda shugabannin jam’iyyun kawance su ka halarta.

Muhammad Bazum ya nuna jin dadinsa ga dukkanin jam’iyyun da suka kulla kawance da shi da kuma shugabanninsu.

A ranar 21 ga watan nan na Febrairu ne za a yi yakin neman zabe karo na biyu tsakanin Muhammadu Bazum da Muhammad Usmanu

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!