Myanmar : Dubban Mutane Sun Fito Kan Tituna Don Yin Tir Da Juyin Mulki

2021-02-07 14:10:43
Myanmar : Dubban Mutane Sun Fito Kan Tituna Don Yin Tir Da Juyin Mulki

Dubban mutanen a manya-manyan biranen kasar Myanmar sun fito kan tituna kwanaki biyu a jere inda suke bukatar sojojin da suka kwace mulki su dawo da mulkin democradiyya da suka rusa a makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa dubban mutane sun fito kan tituna a cibiyar kasuwancin kasar a safiyar yau Lahadi, inda wasunsu na rike da hotunan Firai ministan kasar Aung San Suu kyi da aka yi wa juyin mulki, da kuma tutar jam’iyyarta ta NLD.

A garin Yangon, dubban mutane ne suka fito don yin allawadai da sojojin mulkin, sun kuma bukaci a dawo da tsarin democdiyya a kasar. A wasu garuruwa mutanen sun yi gangami a ofisoshin ‘yansanda a inda suke tsammanin ana tsare da wasu shuwagabannin yan siyasar kasar.

Gwamnatin Sojojin kasar Myanmar dai sun yanke Internet a mafi yawan yankunan kasar sannan sun takaida hanyoyin sadarwa ta wayoyi hanna don duniya kada ta san abinda yake faruwa a kasar. Labarin ya kara da cewa, daliban jami’o’ii da likitoci da kuma sauran yan kasuwa duk sun fito kan tituna, tare da bukatar a dawo da democradiyyar a kasar. Ya zuwa yanzu dai an kama mutane akalla 100 daga cikin masu zanga-zangar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!