​ICC: Alkalai Sun Amince A Gudanar Da Bincike Kan Laifukan Isra’ila A Kan Falastinawa

2021-02-06 19:12:35
​ICC: Alkalai Sun Amince A Gudanar Da Bincike Kan Laifukan Isra’ila A Kan Falastinawa

Alkalan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC sun amince da batun gudanar da bincike kan laifukan yaki da ake zargin Isra’ila ta aikata a kan Falastinawa.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a zaman da manyan alkalan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya suka gudanar a daren jiya, sun amince kan gudanar da bincike kan laifukan da ake zargin Isra’ila ta aikata a kan Falastinawa a cikin yankunansu da ta mamaye tun daga shekara ta 1967.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa, gudanar da irin wannan bincike zai iya bayar da dama a gurfanar da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Isra’ila a gaban kotun manyan laifuka ta duniya.

A nasa bangaren firayi ministan gwamnatin yahudawan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kakkausar suka kan wannan matki na kotun manyan laifuka ta duniya, wanda take shirin dauka kan Isra’ila, inda ya bayyana cewa; wannan ya kara tabbatar da cewa, wannan kotu ta karkata ga siyasa, maimakon gudanar da aikinta bisa kwarewa.

Sai a nata bangaren gwamnatin Falastinawa ta yi lale marhabin da wannan mataki na kotun manyan laifuka ta duniya, inda ta bayyana cewa zata bayar da dukkanin hadin hadin kan da ake bukata domin gudanar da wannan bincike.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!